Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 20:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya amsa maka a ranar wahala!Allah na Yakubu ya kiyaye ka!

2. Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa,Ya kawo maka gudunmawa daga Sihiyona.

3. Ya karɓi hadayunka,Ya kuma ji daɗin dukan sadakokinka.

4. Ya ba ka abin da kake bukata,Ya sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.

5. Mu kuma, sai mu yi sowa ta farin ciki saboda ka ci nasara,Mu yi bikin cin nasara da ka yi,Da yabon Ubangiji Allahnmu.Allah ya amsa dukan roƙe-roƙenka!

6. Yanzu dai na sani Ubangiji yakan ba da nasara ga zaɓaɓɓen sarkinsa,Yakan amsa masa daga samaniyarsa mai tsarki,Da ikonsa mai girma yakan sa shi yă yi nasara.

7. Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara,Waɗansu kuwa ga dawakansu,Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara!

8. Za su yi tuntuɓe su fāɗi,Amma mu za mu tashi mu tsaya daram!

9. Ka ba sarki nasara, ya Ubangiji,Ubangiji zai amsa mana sa'ad da muka yi kira.

Karanta cikakken babi Zab 20