Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 19:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah!Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!

2. Kowace rana tana shelar ɗaukakarsa ga ranar da take biye,Kowane dare yana nanata ɗaukakarsa ga daren da take biye.

3. Ba magana ko kalma da aka hurta,Ba wani amon da aka ji,

4. Duk da haka muryarsu ta game duniya duka,Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya.Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,

5. Tana fitowa kamar ango yana taƙama daga gidansa,Kamar ɗan wasan da ya ƙosa ya yi tsere.

Karanta cikakken babi Zab 19