Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 17:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka kasa kunne ga roƙona, ni adalin mutum,Ka lura da kukana na neman taimako!Ka kasa kunne ga addu'ata,Gama ni ba mayaudari ba ne.

2. Za ka shara'anta shari'ar da za ta gamshe ni,Saboda ka san abin da yake daidai.

3. Ka san zuciyata,Kakan zo gare ni da dare,Ka riga ka jarraba ni sarai,Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba.Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.

4. Zancen aikin sauran mutane,Na yi biyayya ga umarninkaBan bi hanyar rashin hankali ba.

5. Ina tafiya a kan tafarkinka kullum,Ban kuwa kauce ba.

6. Ina addu'a gare ka, ya Allah,Domin kakan amsa mini,Don haka ka juyo wurina ka kasa kunne ga maganata.

7. Ka bayyana ƙaunarka mai banmamaki,Ya Mai Ceto,Muddin muna kusa da kai mun tsira daga maƙiyanmu.

Karanta cikakken babi Zab 17