Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 147:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ba ya jin daɗin ƙarfafan dawakai,Ba ya murna da jarumawan mayaƙa.

11. Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa,Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.

12. Ya Urushalima, ki yabi Ubangiji,Ya Sihiyona, ki yabi Allahnki.

13. Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi,Yakan sa wa jama'arki albarka.

14. Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya,Yakan kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.

15. Yakan ba da umarni,Nan da nan umarnin yakan iso duniya.

16. Yakan aiko da dusar ƙanƙara mai kauri kamar ulu,Ya watsa jaura kamar ƙura.

17. Yakan aiko da ƙanƙara kamar duwatsu,Ba wanda yake iya jurewa da sanyin da yakan aiko!

18. Sa'an nan yakan ba da umarni,Ƙanƙara kuwa ta narke,Yakan aiko da iska, ruwa kuwa yakan gudu.

19. Yana ba Yakubu saƙonsa,Koyarwarsa da dokokinsa kuma ga Isra'ila.

20. Bai yi wa sauran al'umma wannan ba,Domin ba su san dokokinsa ba.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 147