Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 143:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji ka ji addu'ata,Ka kasa kunne ga roƙona!Kai adali ne mai aminci,Don haka ka amsa mini!

2. Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari'a,Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka.

3. Maƙiyina ya tsananta mini,Ya kore ni fata-fata.Ya sa ni a kurkuku mai duhu,Ina kama da waɗanda suka daɗe da mutuwa,

4. Don haka ina niyya in fid da zuciya,Ina cikin damuwa mai zurfi.

5. Na tuna kwanakin baya,Na tuna da dukan abin da ka yi,Na tuna da dukan ayyukanka.

6. Na ɗaga hannuwana sama, ina addu'a gare ka,Kamar busasshiyar ƙasa, raina yana jin ƙishinka.

Karanta cikakken babi Zab 143