Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 139:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Kana kewaye da ni a kowane sashe,Ka kiyaye ni da ikonka.

6. Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana,Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.

7. Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka?Ina zan gudu in tsere maka?

8. Idan na hau cikin samaniya kana can,In na kwanta a lahira kana can,

9. In na tashi sama, na tafi, na wuce gabas,Ko kuma na zauna a can yamma da nisa,

10. Kana can domin ka bi da ni,Kana can domin ka taimake ni.

Karanta cikakken babi Zab 139