Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 139:14-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ina yabonka gama kai abin tsoro ne,Dukan abin da ka yi sabo ne, mai banmamaki.Da zuciya ɗaya na san haka ne.

15. Ka ga lokacin da ƙasusuwana suke siffatuwa,Sa'ad da kuma ake harhaɗa su a hankaliA cikin mahaifiyata,Lokacin da nake girma a asirce.

16. Ka gan ni kafin a haife ni.Ka ƙididdige kwanakin da ka ƙaddara mini,Duka an rubuta su a littafinka,Tun kafin faruwar kowannensu.

17. Ya Allah, tunaninka suna da wuyar ganewa a gare ni,Ba su da iyaka!

18. In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi,Sa'ad da na farka, har yanzu ina tare da kai.

19. Ya Allah, da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye!'Yan ta da zaune tsaye kuma sai su rabu da ni!

20. Suna ambaton mugayen abubuwa a kanka,Suna faɗar mugayen abubuwa gāba da sunanka.

21. Ya Ubangiji, ga yadda nake ƙin waɗanda suke ƙinka,Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maka!

22. Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha,Na ɗauke su, su abokan gābana ne.

23. Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina,Gwada ni, ka gane damuwata.

24. Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni,Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.

Karanta cikakken babi Zab 139