Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 135:4-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ya zaɓar wa kansa Yakubu,Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.

5. Na sani Ubangijinmu mai girma ne,Ya fi dukan alloli girma.

6. Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.

7. Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya,Yakan yi walƙiya domin hadura,Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.

8. A Masar ne ya karkashe 'ya'yan fari na mutane da na dabbobi.

9. A can ne ya aikata mu'ujizai da al'ajabai,Domin ya hukunta Fir'auna da dukan hukumar ƙasarsa.

10. Ya hallakar da sauran al'umma masu yawa,Ya karkashe sarakuna masu iko, wato

11. Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan,Da dukan sarakunan Kan'ana.

12. Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,Ya ba da ita ga Isra'ila.

Karanta cikakken babi Zab 135