Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 135:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Gumakan al'ummai, da azurfa da zinariya aka yi su,Hannuwan mutane ne suka siffata su.

16. Suna da bakuna, amma ba sa magana,Da idanu, amma ba sa gani.

17. Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,Ba kuma numfashi a bakinsu.

18. Ka sa su waɗanda suka yi su,Da dukan waɗanda suke dogara gare su,Su zama kamar gumakan da suka yi!

19. Ku yabi Ubangiji, ya jama'ar Isra'ila,Ku yabe shi, ya ku firistocin Allah!

20. Ku yabi Ubangiji, ya ku Lawiyawa,Ku yabe shi, dukanku da kuke tsoronsa!

21. Ku yabi Ubangiji a Sihiyona da a Urushalima, wato a Haikalinsa.Ku yabi Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 135