Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 135:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yabi Ubangiji!Ku yabi sunansa, ku bayin Ubangiji,

2. Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji,A wuri mai tsarki na Allahnmu.

3. Ku yabi Ubangiji, domin nagari ne shi,Ku raira yabbai ga sunansa, domin shi mai alheri ne.

4. Ya zaɓar wa kansa Yakubu,Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.

5. Na sani Ubangijinmu mai girma ne,Ya fi dukan alloli girma.

6. Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.

7. Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya,Yakan yi walƙiya domin hadura,Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.

8. A Masar ne ya karkashe 'ya'yan fari na mutane da na dabbobi.

9. A can ne ya aikata mu'ujizai da al'ajabai,Domin ya hukunta Fir'auna da dukan hukumar ƙasarsa.

Karanta cikakken babi Zab 135