Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 132:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ka yi wa bawanka Dawuda alkawari,Kada ka rabu da zaɓaɓɓen sarkinka, ya Ubangiji!

11. Ka yi wa Dawuda muhimmin alkawari,Ba kuwa za ka ta da alkawarin ba.Ka ce, “Za naɗa ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza yă zama sarki,Zai yi mulki a bayanka.

12. Idan 'ya'yanka maza za su amince da alkawarina,Da umarnan da na yi musu,'Ya'yansu maza kuma za su bi bayanka su zama sarakuna,A dukan lokaci.”

13. Ubangiji ya yaɓi Sihiyona,A can yake so ya gina Haikalinsa, ya ce,

14. “A nan zan zauna har abada.A nan kuma nake so in yi mulki.

15. Zan tanada wa Sihiyona dukan abin da take bukata a yalwace,Zan ƙosar da matalautanta da abinci.

16. Zan sa firistocinta su yi shela,Cewa ina yin ceto,Jama'ata kuma za su raira waƙa,Suna sowa don farin ciki.

17. A nan ne zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar DawudaYake zama babban sarki,A nan ne kuma zan wanzar daMulkin zaɓaɓɓen sarkina.

18. Zan sa maƙiyansa su sha kunya,Amma mulkinsa zai arzuta.Ya kuma kahu.”

Karanta cikakken babi Zab 132