Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 132:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, kada ka manta da DawudaDa dukan irin aikin da ya yi.

2. Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi,Da rantsuwar da ya yi maka, ya MaÉ—aukaki, Allah na Isra'ila,

3. “Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,

4. Ba zan huta, ko in yi barci ba,

5. Sai sa'ad da na shirya wa Ubangiji wuri,Wato Haikali domin MaÉ—aukaki, Allah na Isra'ila.”

Karanta cikakken babi Zab 132