Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 132:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, kada ka manta da DawudaDa dukan irin aikin da ya yi.

2. Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi,Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra'ila,

3. “Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,

4. Ba zan huta, ko in yi barci ba,

5. Sai sa'ad da na shirya wa Ubangiji wuri,Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra'ila.”

6. Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami,Amma muka same shi a kurmi.

7. Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji,Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”

8. Ka zo wurin hutawarka, ya Ubangiji,Tare da akwatin alkawari,Alama ce ta ikonka.

9. Ka suturta firistoci da adalci,Ka sa dukan jama'arka su yi sowa ta farin ciki!

10. Ka yi wa bawanka Dawuda alkawari,Kada ka rabu da zaɓaɓɓen sarkinka, ya Ubangiji!

11. Ka yi wa Dawuda muhimmin alkawari,Ba kuwa za ka ta da alkawarin ba.Ka ce, “Za naɗa ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza yă zama sarki,Zai yi mulki a bayanka.

Karanta cikakken babi Zab 132