Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 118:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku gode wa Ubangiji,Domin shi mai alheri ne,Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.

2. Bari jama'ar Isra'ila su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”

3. Bari dukan firistoci na Allah su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”

4. Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce,“Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”

5. A cikin wahalata na yi kira ga UbangijiYa kuwa amsa mini, ya kuɓutar da ni.

6. Ubangiji yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba.Me mutane za su iya yi mini?

7. Ubangiji ne yake taimakona,Zan kuwa ga fāɗuwar maƙiyana da idona.

8. Gwamma a dogara ga Ubangiji,Da a dogara ga mutane.

9. Gwamma a dogara ga Ubangiji,Da a dogara ga shugabanni na mutane kawai.

10. Ma ƙiya da yawa sun kewaye ni,Amma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!

11. Suka kewaye ni a kowane gefeAmma na hallaka su ta wurin ikon Ubangiji!

12. Suka rufe ni kamar ƙudan zuma,Amma suka ƙone nan da nan kamar wutar jeji,Ta wurin ikon Ubangiji na hallaka su!

13. Aka auko mini da tsanani,Har aka kore ni,Amma Ubangiji ya taimake ni.

14. Ubangiji yakan ba ni iko, ya ƙarfafa ni,Shi ne Mai Cetona!

15. Ku kasa kunne ga sowar murna ta nasaraA cikin alfarwan jama'ar Allah.“Ikon Ubangiji mai girma ne ya aikata wannan!

16. Ikonsa ne ya kawo mana nasara,Babban ikonsa a wurin yaƙi!”

Karanta cikakken babi Zab 118