Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 116:4-18-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sa'an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce,“Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”

5. Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri,Allahnmu mai rahama ne.

6. Ubangiji yakan kiyaye kāsassu,Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.

7. Kada ki yi shakka, ya zuciyata,Gama Ubangiji yana yi mini alheri.

8. Ubangiji ya cece ni daga mutuwa,Ya share hawayena,Bai bari a kāshe ni ba.

9. Don haka nake tafiya a gaban UbangijiA duniyar masu rai.

10. Na dai yi ta gaskatawa, ko da yakeNa ce, “An ragargaza ni sarai.”

11. Sa'ad da na ji tsoro na ce,“Ba wanda za a iya dogara gare shi.”

12. Me zan bayar ga UbangijiSaboda dukan alheransa gare ni?

13. Zan miƙa hadaya ta sha ga Ubangiji,Ina gode masa domin dā ya cece ni.

14. Zan ba shi abin da na alkawartaA taron dukan jama'arsa.

15. Mutuwar ɗaya daga cikin tsarkakansa,Abu mai daraja ne!

16. Ni bawanka ne, ya Ubangiji,Ina bauta maka yadda mahaifiyata ta yi,Ka 'yantar da ni.

17. Zan miƙa maka hadaya ta godiya,Zan yi addu'ata a gare ka.

18-19. A taron dukan jama'arka,A shirayun Haikalinka,A Urushalima, zan ba ka abin da na alkawarta.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 116