Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 115:8-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ka sa waɗanda suka yi su,Da dukan masu dogara gare su,Su zama kamar gumakan da suka yi!

9. Ku dogara ga Ubangiji, ya ku jama'ar Isra'ila!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

10. Ku dogara ga Ubangiji, ya ku firistoci na Allah!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

11. Ku dogara ga Ubangiji, dukanku waɗanda kuke tsoronsa!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

12. Ubangiji yana tuna da mu, zai kuwa sa mana albarka,Zai sa wa jama'ar Isra'ila albarka,Da dukan firistoci na Allah.

13. Zai sa wa dukan waɗanda suke tsoronsa albarka.Babba da yaro.

14. Ubangiji ya ba ku 'ya'ya,Ku da zuriyarku.

15. Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasaYa sa muku albarka!

Karanta cikakken babi Zab 115