Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 115:14-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ubangiji ya ba ku 'ya'ya,Ku da zuriyarku.

15. Ubangiji, wanda ya yi sama da ƙasaYa sa muku albarka!

16. Samaniya ta Ubangiji ce kaɗai,Amma ya ba mutane duniya.

17. Matacce ba ya yabon Ubangiji,Ko wanda ya gangara zuwa cikin kabari.

18. Amma mu da muke rayayyu, za mu yi masa godiya.A yanzu da har abada.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 115