Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 115:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A gare ka kaɗai, ya Ubangiji,A gare ka kaɗai, ba a gare mu ba,Dole a girmama ka,Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.

2. Me ya sa sauran al'umma suke tambayarmu,“Ina Allahnku?”

3. Allahnmu yana Sama,Yana aikata yadda yake so.

4. Amma nasu alloli na azurfa da zinariya ne,Da hannu aka siffata su.

5. Suna da baki, amma ba sa magana,Suna da idanu, amma ba sa gani.

6. Suna da kunnuwa, amma ba sa ji,Suna da hanci, amma ba sa jin ƙanshi.

7. Suna da hannuwa, amma ba sa iya riƙon kome,Suna da ƙafafu, amma ba sa iya tafiya.Ba su da murya sam.

8. Ka sa waɗanda suka yi su,Da dukan masu dogara gare su,Su zama kamar gumakan da suka yi!

9. Ku dogara ga Ubangiji, ya ku jama'ar Isra'ila!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

10. Ku dogara ga Ubangiji, ya ku firistoci na Allah!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

11. Ku dogara ga Ubangiji, dukanku waɗanda kuke tsoronsa!Shi yake taimakonku, yana kiyaye ku.

Karanta cikakken babi Zab 115