Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 112:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Mai farin ciki ne mutumin da yake tsoron Ubangiji,Mai farin ciki ne shi wanda yake jin daɗin yin biyayya da umarnansa.

2. 'Ya'yansa za su zama manyan ƙasar,Zuriyar mutumin kirki za ta yi albarka.

3. Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya,Adalcinsa zai tabbata har abada.

4. Haske yakan haskaka wa mutanen kirki a cikin duhu,Da waɗanda suke yin alheri, da jinƙai, da gaskiya.

5. Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake,Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya.

6. Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai,Ba za a taɓa mantawa da shi ba.

Karanta cikakken babi Zab 112