Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 111:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Zan yi wa Ubangiji godiya da zuciya ɗaya,A cikin taron jama'arsa.

2. Abubuwan banmamaki ne Ubangiji yake aikatawa!Duk waɗanda suke murna da suSuna so su fahimce su.

3. Dukan abin da yake yi,Cike yake da girma da ɗaukaka,Adalcinsa har abada ne.

4. Ubangiji ba zai bar mu mu manta da ayyukansa masu banmamaki ba,Shi mai alheri ne, mai jinƙai kuma.

5. Yakan tanada wa masu tsoronsa abinci,Bai taɓa mantawa da alkawarinsa ba.

6. Ya nuna ikonsa ga jama'arsaSaboda ya ba su ƙasashen baƙi.

7. Iyakar abin da yake yi duka, da aminci da adalci ne.Dukan umarnansa, abin dogara ne.

8. Sukan tabbata har abada,Da gaskiya da adalci aka ba da su.

Karanta cikakken babi Zab 111