Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 106:34-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Suka ƙi su kashe arna,Yadda Ubangiji ya umarta,

35. Amma suka yi aurayya da su,Suka kwaikwayi halayen arnan.

36. Jama'ar Allah suka yi wa gumaka sujada.Wannan kuwa ya jawo musu hallaka.

37. Suka miƙa 'ya'yansu mata da maza hadaya ga allolin arna.

38. Suka karkashe mutane marasa laifi,Wato 'ya'yansu mata da maza.Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana,Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.

39. Ta wurin ayyukansu, suka ƙazantar da kansu,Suka zama marasa aminci ga Allah.

40. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da jama'arsa,Ransa bai ji daɗinsu ba.

41. Sai ya bar su ƙarƙashin ikon arna,Abokan gābansu suka mallake su.

42. Abokan gābansu suka zalunce su,Suka tilasta su, su yi musu biyayya.

43. Sau da yawa Ubangiji yakan ceci jama'arsa,Amma sun fi so su yi masa tawaye,Suna ta nutsawa can cikin zunubi.

44. Duk da haka Ubangiji ya ji su sa'ad da suka yi kira gare shi,Ya kula da wahalarsu.

45. Saboda su ne ya tuna da alkawarinsa,Ya sāke ra'ayinsa saboda ƙaunarsa mai yawa.

46. Ubangiji ya sa waɗanda suka kama suSu ji tausayinsu.

47. Ka cece mu, ya Ubangiji Allahnmu,Ka komo da mu daga cikin sauran al'umma,Domin mu yabi sunanka mai tsarki,Mu kuma yi murna mu yi maka godiya.

Karanta cikakken babi Zab 106