Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 104:19-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ka halicci wata don ƙididdigar lokatai,Rana kuwa ta san daidai lokacin fāɗuwarta.

20. Ka halicci dare, da duhu inda namomin jeji suke fitowa.

21. Sagarun zakoki sukan yi ruri sa'ad da suke farauta,Suna neman abincin da Allah zai ba su.

22. Sa'ad da rana ta fito,Sai su koma su kwanta a kogwanninsu.

23. Sa'an nan mutane sukan fita su yi aikinsu,Su yi ta aiki har maraice ya yi.

24. Ya Ubangiji, ka halicci abubuwa masu yawa!Da hikima ƙwarai ka halicce su!Duniya cike take da talikanka.

25. Ga babbar teku mai fāɗi,Inda talikai da ba su ƙidayuwa suke zaune,Manya da ƙanana gaba ɗaya.

26. Jiragen ruwa suna tafiya a kansa,Dodon ruwa wanda ka halitta, a ciki yake wasa.

27. Dukansu a gare ka suke dogara,Don ka ba su abinci sa'ad da suke bukata.

28. Ka ba su, sun ci,Ka tanada musu abinci, sun ƙoshi.

29. Sa'ad da ka rabu da su sukan tsorata,In ka zare numfashin da ka ba su, sai su mutu,Su koma turɓaya, da ma da ita aka yi su.

30. Amma sa'ad da ka hura musu numfashi, sai su rayu,Kakan sabunta fuskar duniya.

31. Da ma darajar Ubangiji ta dawwama har abada!Da ma Ubangiji ya yi farin ciki da abin da ya halitta!

32. Ya dubi duniya, sai ta girgiza,Ya taɓa duwatsu, sai suka tuɗaɗo da hayaƙi.

33. Zan raira waƙa ga Ubangiji dukan raina,Zan raira yabbai ga Allah muddin raina.

34. Da ma ya ji daɗin waƙata,Saboda yakan sa ni in yi murna.

35. Da ma a hallakar da masu zunubi daga duniya,Da ma mugaye su ƙare ƙaƙaf!Ka yabi Ubangiji, ya raina!Ka yabi Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 104