Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 103:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka yabi Ubangiji, ya raina!Ka yabi sunansa mai tsarki!

2. Ka yabi Ubangiji, ya raina,Kada ka manta da yawan alherinsa.

3. Ya gafarta dukan zunubaina,Ya kuma warkar da dukan cuce-cucena.

4. Ya cece ni daga kabari,Ya sa mini albarka da ƙauna da jinƙai.

5. Ya cika raina da kyawawan abubuwa,Don in zauna gagau,Ƙaƙƙarfa kamar gaggafa.

6. Ubangiji yakan yi wa waɗanda ake zalunta shari'a ta gaskiya.Yakan ba su hakkinsu.

7. Ya faɗa wa Musa shirye-shiryensa.Ya yardar wa jama'ar Isra'ila su ga manyan ayyukansa.

8. Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma,Mai jinƙirin fushi ne, cike yake da madawwamiyar ƙauna.

9. Ba zai yi ta tsautawa kullum ba,Ba zai yi ta jin haushi har abada ba.

10. Yakan yi mana rangwame sa'ad da yake hukunta mu,Ko sa'ad da yake sāka mana saboda zunubanmu da laifofinmu.

Karanta cikakken babi Zab 103