Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 10:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Yakan ɓuya cikin ƙauyuka,Yă jira a can har yă kashe marasa laifi.Yakan yi sanɗa, ya kama kāsassu,

9. Yakan jira a inda ya ɓuya kamar zaki.Yakan kwanta yana fakon wanda zai kama,Har ya kama shi da tarkonsa ya tafi da shi!

10. Yakan ragargaza kāsasshe,Yă gwada masa ƙarfi, yă ci nasara a kansa.

11. Mugun mutum yakan ce wa kansa, “Allah bai kula ba!Ya rufe idonsa, ba zai taɓa ganina ba.”

12. Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni!Kada ka manta da waɗanda ake zaluntarsu, ya Allah!

13. Yaya mugun zai riƙa raina Allah,Har yă riƙa ce wa kansa, “Ba zai hukunta ni ba”?

14. Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai,Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako.Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka,Gama kullum kakan taimaki masu bukata.

15. Ka karya ikon mugaye, masu mugunta,Ka hukunta su saboda muguntarsu,Har hukuncinsu ya cika sarai.

16. Ubangiji sarki ne har abada abadin,Arna kuma za su ɓace daga ƙasarsa.

17. Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji,Za ka ba su ƙarfin hali.

18. Za ka ji koke-koken waɗanda ake zalunta da na marayu,Ka yi shari'ar da za su ji daɗi,Domin kada 'yan adam su ƙara haddasa wata razana.

Karanta cikakken babi Zab 10