Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 10:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa?Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala?

2. Mugaye suna fāriya, suna kuma tsananta wa matalauta,Ɗana tarkon da suka yi yă kama su.

3. Mugun mutum yana fāriya da mugayen manufofinsa,Mai haɗama yakan zagi Ubangiji ya kuma ƙi shi.

4. Mugun mutum da girmankansa yana cewa, “Ba Allah!”Wannan ne abin da mugu yake tunani.

5. Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.Ba zai fahimci hukuncin Allah ba,Yana yi wa abokan gābansa duban raini.

6. Yana ce wa kansa “Ba zan taɓa fāɗuwa ba,Ba zan taɓa shan wahala ba.”

7. Maganganunsa suna cike da zage-zage, da ƙarairayi, da barazana,Yana da saurin faɗar maganganun ƙiyayya da na mugunta.

8. Yakan ɓuya cikin ƙauyuka,Yă jira a can har yă kashe marasa laifi.Yakan yi sanɗa, ya kama kāsassu,

9. Yakan jira a inda ya ɓuya kamar zaki.Yakan kwanta yana fakon wanda zai kama,Har ya kama shi da tarkonsa ya tafi da shi!

Karanta cikakken babi Zab 10