8. Ifraimu mai tsaro ne a gaban Allahna, annabi kuwa,Duk da haka sun zama kamar mai kafa tarkon kama tsuntsu, a farkon kaka.Akwai ƙiyayya a cikin Haikalin Allahnsu.
9. Sun yi zurfi cikin rashin gaskiyaKamar a kwanakin Gibeya,Ubangiji zai tuna da muguntarsu.Zai hukunta su saboda zunubansu.
10. Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi,Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure,Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al.Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.
11. Darajar Ifraimu za ta tashi kamar tsuntsu,Ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki!