Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 9:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kada ku yi farin cikin, ya mutanen Isra'ila!Kada ku yi murna kamar sauran mutane!Gama kun yi karuwanci, kun rabu da Allahnku.Kuna ƙaunar ijarar karuwanci a kowane masussuka.

2. Masussuka da wurin matsa ruwan inabi ba za su ciyar da su ba.Sabon ruwan inabi kuma ba zai ishe su ba.

3. Ba za su zauna a ƙasar Ubangiji ba,Amma mutanen Ifraimu za su koma Masar.Za su ci haramtaccen abinci a Assuriya.

4. Ba za su yi wa Ubangiji hadaya ta sha ba.Ba za su faranta zuciyarsa da sadakoki ba.Abincinsu zai zama irin na masu makoki.Duk wanda ya ci shi zai haramta.Gama abincinsu zai yi musu maganin yunwa ne kawai,Ba za su kai shi Haikalin Ubangiji ba.

5. Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar idi?Da a ranar idin Ubangiji?

6. Ga shi kuma, suna tafiya zuwa halaka,Masar za ta tattara su,Memfis za ta binne su.Ƙayayuwa za su mallaki abubuwan tamaninsu na azurfa.Sarƙaƙƙiya za ta tsiro a cikin alfarwansu.

7. Ranar hukunci ta zo, ranar ramako ta iso,Isra'ila za ta sani!An ce annabi wawa ne,Mutumin da yake da ruhu kuwa mahaukaci ne,Saboda yawan muguntarku da ƙiyayyarku.

8. Ifraimu mai tsaro ne a gaban Allahna, annabi kuwa,Duk da haka sun zama kamar mai kafa tarkon kama tsuntsu, a farkon kaka.Akwai ƙiyayya a cikin Haikalin Allahnsu.

Karanta cikakken babi Yush 9