Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 7:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Girmankan mutanen Isra'ila ya kai ƙararsu,Duk da haka ba wanda ya komo wurin Ubangiji Allahnsu,Ba su kuwa neme shi ba.

11. Ifraimu kamar kurciya take, marar wayo, marar hankali,Takan tafi Masar da Assuriya neman taimako.

12. Lokacin da suke tafiya, zan shimfiɗa musu ragata,Zan saukar da su ƙasa kamar yadda akan yi wa tsuntsun da yake tashi sama.Zan hukunta su saboda mugayen ayyukansu.

13. “Tasu ta ƙare, gama sun ratse, sun rabu da ni.Halaka za ta auka musu domin sun tayar mini.Ko da yake zan cece su, duk da haka suna faɗar karya a kaina.

14. Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba,Sa'ad da suke kuka a gadajensu,Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi.Sun yi mini tawaye.

15. Ko da yake na horar da su, na ƙarfafa damatsansu,Duk da haka suna shirya mini maƙarƙashiya.

16. Sun juya mini baya, suna bin gunkin nan Ba'al.Suna kama da tankwararren baka.Za a kashe shugabanninsu da takobiSaboda maganganunsu na fariya.Za su zama abin ba'a a ƙasar Masar.”

Karanta cikakken babi Yush 7