Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 6:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji,Gama shi ne ya yayyaga,Shi ne kuma zai warkar.Shi ne ya yi mana rauni,Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.

2. Bayan kwana biyu zai rayar da mu.A rana ta uku kuwa zai tashe muMu yi zammanmu a gabansa.

3. Mu nace domin mu san UbangijiZuwansa tabbatacce ne kamar wayewar gari.Zai zo wurinmu kamar ruwan sama,Kamar ruwan bazara da yake shayar da ƙasa.”

4. Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu?Me zan yi da ke, ya Yahuza?Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi,Kamar kuma raɓar da take watsewa da wuri.

5. Domin haka na sassare su ta wurin annabawansu,Na karkashe su da maganar bakina.Hukuntaina suna kama da hasken da yake ketowa.

6. Gama ƙauna nake so, ba sadaka ba,Sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.

Karanta cikakken babi Yush 6