Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 5:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. “Ayyukansu ba su bar suSu koma wurin Allahnsu ba,Gama halin karuwanci yana cikinsu,Don haka kuma ba su san Ubangiji ba.

5. Girmankan mutanen Isra'ila yana ba da shaida a kansu.Mutanen Ifraimu za su yi tuntuɓe cikin laifinsu.Mutanen Yahuza kuma za su yi tuntuɓe tare da su.

6. Da garkunan tumaki da na awaki, da na shanunsuZa su tafi neman Ubangiji,Amma ba za su same shi ba,Gama ya rabu da su.

7. Sun ci amanar Ubangiji.Su haifi shegu.Yanzu amaryar wata za ta cinye su da gonakinsu.

Karanta cikakken babi Yush 5