Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 4:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Za su ci, amma ba za su ƙoshi ba.Za su yi karuwanci, amma ba za su ƙaru ba.Gama sun rabu da Ubangiji don su bauta wa gumaka.

11. “Karuwanci, da ruwan inabi,Da ruwan inabin da bai sa hauka ba sukan kawar da hankali.

12. Mutanena sukan yi tambaya a wurin abin da aka yi da itace,Sandansu yakan faɗa musu gaiɓu,Gama ruhun karuwanci ya ɓad da su,Sun rabu da Allahnsu don su yi karuwanci.

13. Suna miƙa sadaka a bisa ƙwanƙolin duwatsu.Suna yin hadaya a bisa tuddai,Da kuma a gindin itacen oak, da aduruku, da katambiri,Domin suna da inuwa mai kyau.Don haka 'ya'yanku mata suke karuwanci,Surukanku mata suke yin zina.

14. Ba zan hukunta 'ya'yanku mata sa'ad da suka yi karuwanci ba,Ko kuwa surukanku mata sa'ad da suka yi zina ba,Gama mazan da kansu sukan shiga wurin karuwai.Sukan miƙa sadaka tare da karuwai a Haikali,Mutane marasa fahimi za su lalace.

15. “Ko da yake mutanen Isra'ila suna karuwanci,Kada kuma mutanen Yahuza su yi laifi.Kada ku tafi Gilgal,Ko ku haura zuwa Bet-awen.Kada ku yi rantsuwa da cewa,‘Har da zatin Ubangiji!’

16. Mutanen Isra'ila masu taurinkai ne kamar alfadari.Ta yaya Ubangiji zai yi kiwonsuKamar 'ya'yan tumaki a makiyaya mai fāɗi?

17. Mutanen Ifraimu sun haɗa kai da gumaka,Sai a rabu da su.

18. Su taron mashaya ne kawai,Karuwai ne kuma.Suna ƙaunar abin kunya.

19. Iska ta ƙunshe su cikin fikafikanta.Za su ji kunyar bagadansu.”

Karanta cikakken babi Yush 4