Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 13:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Ifraimu ta yi magana, mutane suka yi rawar jiki. An ɗaukaka ta cikin Isra'ila,Amma ta yi laifi ta wurin bauta gunkin nan Ba'al,Ta kuwa mutu.

2. Har yanzu suna ta ƙara yin zunubi,Suna yi wa kansu gumaka na zubi,Da gwaninta sukan yi gumaka da azurfarsu,Dukansu aikin hannu ne.Sukan ce, “Ku miƙa wa waɗannan hadayu!”Mutane sukan sumbaci siffofin maruƙa.

3. Don haka za su zama kamar ƙāsashin da akan yi da safe,Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri.Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka,Ko kuwa kamar hayaƙin da yake fita ta bututu.

4. Ubangiji ya ce, “Ni ne Ubangiji AllahnkuTun daga ƙasar Masar.Banda ni ba ku san wani Allah ba,Banda ni kuma ba wani mai ceto.

5. Ni ne wanda ya san ku a cikin jeji,A ƙasar da take da ƙarancin ruwan sama.

6. Sa'ad da suka sami wurin kiwo, suka ƙoshi,Sai suka yi girmankai,Suka manta da ni.

7. Zan zama musu kamar zaki,Kamar damisa zan yi kwanto a gefen hanya.

8. Zan auka musu kamar beyar,Wadda aka ƙwace mata 'ya'ya.Zan yage ƙirjinsu, in cinye su kamar zaki,Kamar mugun naman jeji zan yayyage su.

Karanta cikakken babi Yush 13