Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 10:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Isra'ila kurangar inabi ce mai bansha'awaWadda yake ba da 'ya'ya da yawa.Ƙara yawan arzikinsu,Ƙara gina bagadansu.Ƙara yawan wadatar ƙasarsu.Ƙara kyautata ginshiƙansu.

2. Zuciyarsu ta munafunci ce,Yanzu tilas za su ɗauki hakkin laifinsu,Ubangiji zai farfashe bagadansu da ginshiƙansu.

3. Gama yanzu za su ce,“Ba mu da sarki,Domin ba mu ji tsoron Ubangiji ba.Amma me sarki zai yi mana?”

4. Surutai kawai suke yi,Suna yin alkawaran ƙarya,Don haka hukunci zai zaburo kamar muguwar ciyawa mai dafi a kunyoyin gona.

5. Mazaunan Samariya suna rawar jikiDomin ɗan maraƙin Bet-awen,Mutane za su yi makoki dominsa,Firistoci matsafa, za su yi kururuwa dominsa,Da kuma darajarsa wadda ta rabu da shi.

6. Za a kai ɗan maraƙin a AssuriyaDon a biya wa sarki haraji.Za a kunyatar da Ifraimu,Isra'ila kuwa za ta ji kunya saboda shawararta.

7. Sarakunan Samariya za su ɓace,Kamar kumfa a bisa ruwa.

8. Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi,Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu.Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!”Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”

9. Ubangiji ya ce, “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra'ila!Tun daga wancan lokaci kuka yi ta ci gaba.Ashe, yaƙi ba zai tarshe su a Gibeya ba?

Karanta cikakken babi Yush 10