Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 3:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya sāke ce wa Yunusa,

2. “Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi musu shelar saƙon da zan faɗa maka.”

3. Sai Yunusa ya tashi ya tafi Nineba kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa. Nineba kuwa babban birni ne. Zai kai mutum tafiyar kwana uku kafin yă ƙure birnin.

4. Sai Yunusa ya kama tafiya yana ratsa birnin, da ya yi tafiyar yini guda, sai ya yi shela ya ce, “Nan da kwana arba'in za a hallaka Nineba.”

5. Sai mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka tsai da shawara, cewa kowa da kowa ya yi azumi. Dukan mutane kuwa babba da yaro, suka sa tufafin makoki.

Karanta cikakken babi Yun 3