Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yow 3:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza 'ya'yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”

9. Ku sanar wa al'ummai da wannan,Su yi shirin yaƙi,Su kira mayaƙa!Su tattaro sojoji, su zo!

10. Su bubbuge allunan garmunansu,Su yi takuba da su.Su ƙera māsu da wuƙaƙen da akeyi wa itatuwa aski.Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumine!”

11. Su gaggauta, su zo su al'ummai dasuke kewaye,Su tattaru a kwarin.“Ya Ubangiji, ka saukar darundunarka mai ƙarfi.”

12. “Sai al'ummai su yi shiri,Su zo kwarin Yehoshafat,Gama a can zan zauna in shara'antaal'umman da suke kewaye,

13. Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi.Su shiga su tattaka,Gama wurin matsewar ruwan inabiya cika.Manyan randuna sun cika sunatumbatsa,Gama muguntarsu da yawa take.”

14. Dubun dubbai suna cikin kwarin daza a yanke shari'a!Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa akwarin yanke shari'a.

15. Rana da wata sun yi duhu,Taurari kuma ba su haskakawa.

16. Ubangiji yana magana da ƙarfi dagaSihiyona,Yana tsawa daga Urushalima,Sammai da duniya sun girgiza.Amma Ubangiji shi ne mafakarjama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.

Karanta cikakken babi Yow 3