Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yow 3:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi.Su shiga su tattaka,Gama wurin matsewar ruwan inabiya cika.Manyan randuna sun cika sunatumbatsa,Gama muguntarsu da yawa take.”

14. Dubun dubbai suna cikin kwarin daza a yanke shari'a!Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa akwarin yanke shari'a.

15. Rana da wata sun yi duhu,Taurari kuma ba su haskakawa.

16. Ubangiji yana magana da ƙarfi dagaSihiyona,Yana tsawa daga Urushalima,Sammai da duniya sun girgiza.Amma Ubangiji shi ne mafakarjama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.

17. “Sa'an nan za ku sani ni ne UbangijiAllahnku,Wanda yake zaune a Sihiyona, tudunatsattsarka.Urushalima kuma za ta tsarkaka,Sojojin abokan gāba ba za su ƙararatsawa ta cikinta ba.

18. “A wannan lokaci tsaunuka za su rufuda kurangar inabi,Tuddai za su cika da shanu,Dukan rafuffukan Yahuza za sugudano da ruwa,Maɓuɓɓuga za ta gudano dagaHaikalin Ubangiji,Ta shayar da kwarin Shittim.

19. “Masar za ta zama hamada,Edom kuma za ta zama kufai,Saboda kama-karya da suka yi wamutanen Yahuza,Saboda sun zubar da jinin marasalaifi a ƙasarsu,

20. Za a zauna a Yahuza da Urushalimadukan tsararraki har abada.

21. Zan sāka alhakin jininsu,Ba zan kuɓutar da mai laifi ba,Gama Ubangiji yana zaune a Sihiyona.”Sihiyona.”

Karanta cikakken babi Yow 3