Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 2:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na'omi tana da wani dangin mijinta, Elimelek, sunansa Bo'aza, shi kuwa attajiri ne.

2. Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.”Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.”

3. Rut ta tafi wata gona, tana bin bayan masu girbi, tana kala. Ta yi sa'a kuwa ta fāɗa a gonar Bo'aza, dangin Elimelek.

4. Sai ga Bo'aza ya zo daga Baitalami, ya ce wa masu girbi, “Salamu alaikun.”Suka amsa, “Alaika salamu.”

5. Sa'an nan Bo'aza ya tambayi baransa da yake shugaban masu girbin, ya ce, “'Yar wace ce wannan?”

6. Baran ya ce, “Ita 'yar Mowab ce wadda ta zo tare da Na'omi daga ƙasar Mowab.

Karanta cikakken babi Rut 2