Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 1:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Inda za ki rasu, ni ma can zan rasu, a binne ni. Idan na bar wani abu ya raba ni da ke, in dai ba mutuwa ba, to, Ubangiji ya yi mini hukunci mai zafi!”

18. Da Na'omi ta ga Rut ta ƙudura ta tafi tare da ita, sai ta ƙyale ta.

19. Su biyu kuwa suka kama hanya har suka isa Baitalami. Da suka isa Baitalami, sai dukan garin ya ruɗe saboda su. Mata suka ce, “Na'omi ce wannan?”

20. Ita kuwa ta ce musu, “Kada ku kira ni Na'omi, wato mai farin ciki, sai dai Mara, wato mai baƙin ciki, gama Mai Iko Dukka ya wahalshe ni ƙwarai.

21. Na tafi a wadace, ga shi, Ubangiji ya komo da ni hannu wofi. Don me kuke kirana mai farin ciki da yake Ubangiji Mai Iko Dukka ya wahalshe ni, ya kuma aukar mini da masifa?”

22. Haka Na'omi ta koma daga ƙasar Mowab tare da surukarta Rut, mutuniyar Mowab. Suka isa Baitalami a farkon kakar sha'ir.

Karanta cikakken babi Rut 1