Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Oba 1:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Girmankanki ya yaudare ki,Kina zaune a kagara, a kan dutse,Wurin zamanki yana canƙwanƙolin duwatsu.Don haka a zuciya kike cewa,‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’

4. Ko da yake kina shawagi can samakamar gaggafa,Gidanki kuma yana can cikin taurari,Daga can zan saukar da ke,” in jiUbangiji

5. “Idan ɓarayi sun shiga gidanki,Idan kuma 'yan fashi sun shigagidanki da dare,Yaya za su washe ki?Za su sace abin da ya ishe su nekaɗai,Idan kuma ɓarayin 'ya'yan inabisun shiga gonar inabinki,Za su bar miki kala kurum.

6. Isuwa, wato Edom, ga taskarka,An washe ta ƙaƙaf!

7. Waɗanda kake amana da su,Za su kore ka daga ƙasarka.Mutanen da suke amana da kai,Za su yaudare ka,Su ci ka da yaƙi.Abokan nan naka da kake ci tare dasu za su kafa maka tarko,Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayonnan nasa?’ ”

8. Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zanhukunta Edom,Zan hallaka masu hikimarka,Zan shafe hikima daga dutsenIsuwa.

9. Jarumawanka za su firgita, yaTeman,Za a kashe kowane mutum dagadutsen Isuwa.

Karanta cikakken babi Oba 1