Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Oba 1:18-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Jama'ar Yakubu za ta zama kamarwuta,Jama'ar Yusufu kuwa kamarharshen wuta,Jama'ar Isuwa za ta zama kamartattaka.Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zaitsira.Ni Ubangiji na faɗa.”

19. Isra'ilawan da yake Negeb za sumallaki dutsen Isuwa,Waɗanda suke a filaye na Yahuza za sumallaki ƙasar Filistiya.Isra'ilawa za su mallaki yankinƙasar Ifraimu da Samariya,Jama'ar Biliyaminu za su mallakiGileyad.

20. Rundunar masu zaman talala naIsra'ilawaZa su mallaki Kan'aniyawa har zuwaZarefat.Masu zaman talala na Urushalima dasuke a SefaradZa su mallaki biranen Negeb.

21. Isra'ilawa za su hau DutsenSihiyona, su cece shi,Za su mallaki dutsen Isuwa,Ubangiji ne Sarki.

Karanta cikakken babi Oba 1