Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Oba 1:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Ranar da ni Ubangiji zanshara'anta al'ummai duka ta zokusa,Ke, Edom, abin da kika yi,Shi ne za a yi miki.Ayyukanki za su koma a kanki.

16. Kamar yadda kuka sha hukunci akan tsattsarkan dutsena,Haka dukan sauran al'umma za su yita sha.Za su sha, su yi tangaɗi,Su zama kamar ba su taɓa kasancewaba.”

17. “Amma za a sami waɗanda za sutsira daga Dutsen Sihiyona,Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki.Jama'ar Yakubu za ta mallakimallakarta.

18. Jama'ar Yakubu za ta zama kamarwuta,Jama'ar Yusufu kuwa kamarharshen wuta,Jama'ar Isuwa za ta zama kamartattaka.Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zaitsira.Ni Ubangiji na faɗa.”

19. Isra'ilawan da yake Negeb za sumallaki dutsen Isuwa,Waɗanda suke a filaye na Yahuza za sumallaki ƙasar Filistiya.Isra'ilawa za su mallaki yankinƙasar Ifraimu da Samariya,Jama'ar Biliyaminu za su mallakiGileyad.

20. Rundunar masu zaman talala naIsra'ilawaZa su mallaki Kan'aniyawa har zuwaZarefat.Masu zaman talala na Urushalima dasuke a SefaradZa su mallaki biranen Negeb.

21. Isra'ilawa za su hau DutsenSihiyona, su cece shi,Za su mallaki dutsen Isuwa,Ubangiji ne Sarki.

Karanta cikakken babi Oba 1