Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 9:21-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Ka taimake su a jeji shekara arba'in,Ka ba su dukan abin da suke bukata,Ƙafafunsu ba su kumbura su yi musu ciwo ba.

22. “Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi,Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu.Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon,Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.

23. Ka riɓaɓɓanya zuriyarsu kamar taurarin sararin sama,Ka sa suka ci ƙasar, suka zauna cikinta,Ƙasar da aka yi wa kakanninsu alkawari za ka ba su.

24. Saboda haka zuriyarsu suka shiga, suka mallaki ƙasar Kan'ana.Ka rinjayi mutanen da suke zama a can.Ka ba jama'arka iko su yi yadda suke soDa mutane, da sarakunan ƙasar Kan'ana.

25. Sun ci birane masu garu, da ƙasa mai dausayi,Da gidaje cike da dukiya, da rijiyoyi, da gonakin inabi,Da itatuwan zaitun, da itatuwa masu 'ya'ya.Suka ci dukan abin da suke so, suka yi taiɓa,Suka mori dukan kyawawan abubuwan da ka ba su.

26. “Amma suka yi maka rashin biyayya, suka tayar maka,Suka juya wa dokokinka baya,Suka karkashe anna bawan da suka faɗakar da su,Waɗanda suka faɗa musu su juyo gare ka.Suka yi ta saɓa maka lokaci lokaci.

27. Saboda haka ka bar abokan gābansu su ci su, mallake su.A wahalarsu sun yi kira gare ka domin taimako,Ka kuwa amsa musu daga Sama.Ta wurin jinƙanka mai yawa ka aiko musu da shugabanni,Waɗanda suka kuɓutar da su daga maƙiyansu.

28. Sa'ad da zaman salama ya komo, sai kuma su yi zunubi,Kai kuma sai ka bar abokan gabansu su ci su.Duk da haka idan sun tuba, suka roƙe ka ka cece su,Kakan ji daga Sama,sau da yawa,Ka cece su da jinƙanka mai yawa.

29. Ka gargaɗe su su yi biyayya da koyarwarka,Amma sun bijire wa dokoki saboda girmankai,Ko da yake kiyaye dokarka ita ce hanyar rai.Masu taurinkai sun taurare, sun ƙi yin biyayya.

30. “Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su,Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne.Saboda haka ka sa waɗansu al'ummai su mallaki jama'arka.

31. Duk da haka, saboda yawan jinƙanka,Ba ka yashe su ko ka hallaka su ba.Kai Allah mai alheri ne mai jinƙai!

32. “Ya Allah, Allahnmu, da girma kake!Kai mai banrazana ne, cike da iko!Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta.Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu,Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba!Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu,Da annabawanmu, da kakanninmu,Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala.Ka san irin wahalar da muka sha.

33. Ka yi daidai da ka hukunta mu haka!Kai mai aminci ne, mu kuwa mun yi zunubi.

34. Gama kakanninmu, da sarakunanmu,Da shugabanninmu, da firistocinmu,Ba su kiyaye dokarka ba.Ba su kasakunne ga umarnanka da gargaɗinka ba.Da waɗannan ne kake zarginsu.

35. Da albarkacinka sarakuna suke mulkin jama'arka,Sa'ad da suke ƙasashen waje, ƙasa mai dausayi ka ba su,Amma ba su juyo su bar zunubi, su bauta maka ba.

36. Ga shi, a yau mu bayi ne a ƙasar da ka ba mu,Wannan ƙasa mai dausayi wadda take ba mu abinci.

37. Amfanin ƙasa duk yana tafiya ga sarakunanDa ka ɗora su a kanmu saboda mun yi zunubi.Suna yi mana yadda suka ga dama, mu da dabbobinmu,Muna cikin baƙin ciki.”

38. “Saboda wannan duka muke yin alkawari mai ƙarfi a rubuce. Shugabanninmu kuwa, da Lawiyawanmu, da firistocinmu, suka buga hatimi, suka sa hannu.”

Karanta cikakken babi Neh 9