Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 8:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan jama'a suka taru wuri ɗaya a filin Ƙofar Ruwa, suka faɗa wa Ezra, magatakarda, ya kawo Attaura ta Musa wanda Ubangiji ya ba Isra'ilawa.

2. A ran ɗaya ga watan bakwai, sai Ezra, firist, ya kawo Attaura a gaban taron jama'a, mata da maza, da dukan waɗanda za su ji, su fahimta.

3. Ya karanta Littafin, yana fuskantar filin Ƙofar Ruwa, a gaban mata da maza, da waɗanda za su iya fahimta. Mutane duka kuwa suka kasa kunne ga karatun Attaura, tun da sassafe har zuwa rana tsaka.

4. Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.

5. Ezra kuwa ya buɗe Littafin a gaban jama'a duka, domin yana sama da jama'a. Sa'ad da ya buɗe Littafin, sai jama'a duka suka miƙe tsaye.

6. Sai Ezra ya yabi Ubangiji Allah Maɗaukaki.Jama'a duka suka amsa, “Amin, amin!” suna ɗaga hannuwansu. Suka sunkuyar da kansu har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada.

Karanta cikakken babi Neh 8