Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 6:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Gama dukansu so suke su tsoratar da mu, suna cewa, “Za su daina aikin.” Amma na yi addu'a, na ce, “Ya Allah, ka ƙarfafa ni.”

10. Sa'ad da na ziyarci Shemaiya ɗan Delaiya, wato jikan wanda aka hana shi fita, sai ya ce mini, “Bari mu tafi cikin Haikalin Allah, mu rufe ƙofofin Haikalin, gama suna zuwa su kashe ka, za su iya zuwa a wani dare su kashe ka.”

11. Sai na ce, “Mutum kamata ne, zai gudu? Mutum irina zai shiga Haikali don ya tsere? To, ba zan tafi ba.”

12. Na gane Allah bai aike shi wurina ba. Ya yi mini wannan magana domin Tobiya da Sanballat sun haɗa baki da shi.

13. Gama da wannan nufi ne suka haɗa baki, don in ji tsoro, in yi yadda suke so, in yi zunubi, da haka za su ba ni mugun suna, su yi mini ba'a.

14. “Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat bisa ga abubuwan nan da suka yi, da annabiya Nowadiya, da sauran annabawa waɗanda suka so su tsoratar da ni.”

15. A cikin kwana hamsin da biyu aka gama garun, ran ashirin da biyar ga watan Elul.

16. Sa'ad da abokan gābanmu da dukan al'umman da suke kewaye da mu suka ji, sai suka ji tsoro, gabansu kuma ya faɗi, gama sun gane, da taimakon Allahnmu muka yi wannan aiki.

17. A kwanakin nan kuma shugabannin Yahuza suka yi ta aika wa Tobiya da wasiƙu, shi kuma Tobiya yana ta aika musu da nasa wasiƙu.

18. Mutane da yawa a Yahuza sun rantse za su goyi bayan Tobiya, domin ya auri 'yar Shekaniya, ɗan Ara. Ɗansa kuma, wato Yohenan, ya auri 'yar Meshullam, ɗan Berikiya.

19. Mutane suka yi magana a kan ayyukan kirki na Tobiya a gabana. Suka kuma kai maganata a wurinsa, sai Tobiya ya yi ta aika mini da wasiƙu don ya tsoratar da ni.

Karanta cikakken babi Neh 6