Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 5:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Akwai waɗanda suka ce, “Mu da 'ya'yanmu mata da maza muna da yawa, sai mu sami hatsi don mu ci mu rayu.”

3. Waɗansu kuma suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”

4. Akwai waɗansu kuma da suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.

5. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, 'ya'yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duka da haka muna tilasta wa 'ya'yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma waɗansu daga cikin 'ya'yanmu mata an riga an bautar da su, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”

6. Ni Nehemiya na husata ƙwarai, sa'ad da na ji kukansu da wannan magana.

7. Sai na yi shawara a zuciyata, na yi wa manya da shugabanni faɗa, na ce musu, “Kuna musguna wa 'yan'uwanku da yake kuna ba su rance da ruwa.”Sa'an nan na kira babban taro saboda su.

8. Na ce musu, “Da iyakacin ƙoƙarinmu mun fanshi 'yan'uwanmu Yahudawa waɗanda aka sayar wa al'ummai, amma ga shi, kuna tilasta wa 'yan'uwanku su sayar da kansu ga 'yan'uwansu.” Sai suka yi tsit, suka rasa abin da za su ce.

9. Na kuma ce musu, “Abin da kuke yi ba shi da kyau. Ya kamata ku yi tsoron Allah don ku hana al'ummai, abokan gabanmu, yi mana ba'a.

10. Ni ma da 'yan'uwana da barorina muna ba da rancen kuɗi da hatsi. Sai mu daina sha'anin ba da rance da ruwa.

11. Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”

Karanta cikakken babi Neh 5