Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 4:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Sanballat ya ji muna ginin garun, sai ya husata ƙwarai, ya yi wa Yahudawa ba'a.

2. Ya yi magana a gaban 'yan'uwansa da sojojin Samariya ya ce, “Mene ne waɗannan Yahudawa kumamai suke yi? Za su mai da abubuwa yadda suka a dā ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama ginin a rana ɗaya ne? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?”

3. Tobiya Ba'ammone yana kusa da shi, ya ce, “Ai, garun da suke ginawa da duwatsu, ko dila ya hau, sai ya rushe shi!”

4. Sai ni, Nehemiya, na yi addu'a, na ce, “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana raina mu, ka sa ba'arsu ta koma kansu, ka sa a washe su a kai su ƙasar bauta.

5. Kada ka shafe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.”

6. Muka gina garun, har ya kai rabin tsayinta, domin mutane sun himmatu da aikin.

7. Amma sa'ad da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da mutanen Ashdod, suka ji yadda ginin garun Urushalima yake ci gaba, ana kuma tattoshe tsattsaguwa, sai suka husata.

8. Dukansu suka ƙulla za su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su ta da hankali a cikinta.

9. Sai muka yi addu'a ga Allahnmu, muka sa masu tsaro su yi mana tsaro dare da rana saboda su.

10. Mutanen Yahuza kuwa suka ce,“Ƙarfin ma'aikata yana kāsawa,Akwai komatsai da yawa da za a kwashe,Yaya za mu iya gina garun yau?”

11. Abokan gābanmu kuma suka ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.”

12. Da Yahudawan da suke zaune kusa da su suka zo, suka yi ta nanata mana irin shirin abokan gabanmu, wato za su zo su fāɗa mana.

Karanta cikakken babi Neh 4