Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 13:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A wannan rana aka karanta daga littafin Musa a kunnuwan jama'a. A cikinsa aka tarar da inda aka rubuta, cewa kada Ba'ammone, ko mutumin Mowab ya shiga taron jama'ar Allah.

2. Gama ba su taryi jama'ar Isra'ila da abinci da abin sha ba, amma suka yi ijara da Bal'amu ya zo ya la'anta musu su, amma Allahnmu ya juyar da la'anar ta zama albarka.

3. Da mutane suka ji dokokin, sai suka ware dukan waɗanda suke ba Isra'ilawa ba.

4. Kafin wannan lokaci Eliyashib, firist, wanda aka sa shi shugaban ɗakunan ajiya na Haikalin Allahnmu, wanda yake da dangantaka da Tobiya,

5. ya shirya wa Tobiya babban ɗaki inda dā aka ajiye hadaya ta gari, da turare, da tasoshi, da zakar hatsi, da ruwan inabi, da mai, waɗanda aka umarta a ba Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da inda aka ajiye sadakokin da ake ba firistoci.

6. Ba na nan a Urushalima sa'ad da wannan abu ya faru, gama a shekara ta talatin da biyu ta sarautar Artashate, Sarkin Babila, na tafi wurin sarki. Daga baya sarki ya ba ni izini in koma.

7. Da na komo Urushalima, sai na ga mugun abin da Eliyashib ya yi domin Tobiya, yadda ya shirya masa ɗaki a filin Haikalin Allah.

8. Sai na husata ƙwarai, na fitar da kayan ɗakin Tobiya a waje.

9. Sai na umarta, suka kuwa tsarkake ɗakunan, sa'an nan na mayar da tasoshin Haikalin Allah, da hadaya ta gari, turare a ciki.

10. Na kuma iske ba a ba Lawiyawa rabonsu ba. Saboda wannan Lawiyawa da mawaƙa masu hidima suka watse zuwa gonakinsu.

11. Sai na yi wa shugabanni faɗa, na ce, “Me ya sa aka ƙi kula da Haikalin Allah?” Sa'an nan na tara Lawiyawa da mawaƙa, na sa su a wuraren aikinsu.

12. Sai dukan mutanen Yahuza suka kawo zakar hatsi, da ta ruwan inabi, da ta mai, a ɗakunan ajiya.

Karanta cikakken babi Neh 13