Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 12:1-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Firistoci da Lawiyawa da suka komo tare da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa, su neSeraiya, da Irmiya, da Ezra,

2-7. Amariya, da Malluki, da Hattush,Shekaniya, da Rehum, da Meremot,Iddo, da Ginneton, da Abaija,Miyamin, da Mawadiya, da Bilga,Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya,Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya.Waɗannan su ne shugabannin firistoci da 'yan'uwansu a zamanin Yeshuwa.

8-9. Lawiyawa su ne,Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel,Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da 'yan'uwansa.Bukbukiya da Unno, 'yan'uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada.

10. Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada.

11. Yoyada ya haifi Jonatan, Jonatan ya haifi Yadduwa.

12-21. A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci,na wajen Seraiya, Meraiya nena wajen Irmiya, Hananiya nena wajen Ezra, Meshullam nena wajen Amariya, Yehohanan nena wajen Malluki, Jonatan nena wajen Shebaniya, Yusufu nena wajen Harim, Adana nena wajen Merayot, Helkai nena wajen Iddo, Zakariya nena wajen Ginneton, Meshullam nena wajen Abaija, Zikri nena wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai nena wajen Bilga, Shimeya nena wajen Shemaiya, Yehonatan nena wajen Yoyarib, Mattenai nena wajen Yedaiya, Uzzi nena wajen Sallai, Kallai nena wajen Amok, Eber nena wajen Hilkiya, Hashabiya nena wajen Yedaiya, Netanel ne

22. A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.

23. Aka kuma rubuta shugabannin gidajen kakannin zuriyar Lawi a tarihi, har zuwa zamanin Yohenan ɗan Eliyashib.

24. Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.

25. Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi.

26. Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda.

Karanta cikakken babi Neh 12