Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 11:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shugabannin jama'a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama'a kuma suka jefa kuri'a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa.

2. Jama'a suka sa wa dukan waɗanda suka tafi su zauna a Urushalima da yardar ransu albarka.

3. Waɗannan su ne shugabannin lardi waɗanda suka zauna a Urushalima, amma a garuruwan Yahuza kowa ya zauna a mahallinsa a garuruwansu, wato Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da ma'aikatan Haikali, da zuriyar barorin Sulemanu.

4. Waɗansu mutanen Yahuza da na Biliyaminu suka zauna a Urushalima.Daga cikin mutanen Yahuza akwai Ataya ɗan Azariya, wato jīkan Zakariya ɗan Amariya. Sauran kakanninsa su ne Shefatiya, da Mahalalel, zuriyar Feresa ɗan Yahuza.

5. Akwai kuma Ma'aseya ɗan Baruk, jīkan Kolhoze. Sauran kakanninsa su ne Hazaiya, da Adaya, da Yoyarib, da Zakariya, zuriyar Shela ɗan Yahuza.

Karanta cikakken babi Neh 11