Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 11:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shugabannin jama'a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama'a kuma suka jefa kuri'a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa.

2. Jama'a suka sa wa dukan waɗanda suka tafi su zauna a Urushalima da yardar ransu albarka.

3. Waɗannan su ne shugabannin lardi waɗanda suka zauna a Urushalima, amma a garuruwan Yahuza kowa ya zauna a mahallinsa a garuruwansu, wato Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da ma'aikatan Haikali, da zuriyar barorin Sulemanu.

4. Waɗansu mutanen Yahuza da na Biliyaminu suka zauna a Urushalima.Daga cikin mutanen Yahuza akwai Ataya ɗan Azariya, wato jīkan Zakariya ɗan Amariya. Sauran kakanninsa su ne Shefatiya, da Mahalalel, zuriyar Feresa ɗan Yahuza.

5. Akwai kuma Ma'aseya ɗan Baruk, jīkan Kolhoze. Sauran kakanninsa su ne Hazaiya, da Adaya, da Yoyarib, da Zakariya, zuriyar Shela ɗan Yahuza.

6. Dukan mutanen Feresa da suka zauna Urushalima su ɗari huɗu da sittin da takwas ne, dukansu kuwa muhimman mutane ne.

7. Waɗannan su ne mutanen Biliyaminu, Sallai ɗan Meshullam, jīkan Yowed. Sauran kakanninsa su ne Fedaiya, da Kolaiya, da Ma'aseya, da Itiyel da Yeshaya.

8. Sa'an nan kuma ga Gabbai da Sallai danginsa, mutum ɗari tara da ashirin da takwas.

9. Yowel ɗan Zikri shi ne shugabansu, Yahuza ɗan Hassenuwa shi ne shugaba na biyu cikin birnin.

10. Na wajen firistoci, su ne Yedaiya ɗan Yoyarib, da Yakin,

11. da Seraiya ɗan Hilkiya, jīkan Shallum. Sauran kakanninsa, su ne Zadok, da Merayot, da Ahitub, mai lura da Haikalin Allah.

12. Tare da 'yan'uwansu waɗanda suka yi aiki a Haikali, su ɗari takwas da ashirin da biyu ne.Akwai kuma Adaya ɗan Yeroham, jīkan Felaliya. Sauran kakanninsa su ne Amzi, da Zakariya, da Fashur, da Malkiya.

13. Tare da 'yan'uwansu shugabannin gidajen kakanni, su ɗari da arba'in da biyu. Sai kuma Amashai ɗan Azarel, jīkan Azai. Sauran kakanninsa su ne Meshillemot, da Immer.

14. Tare da 'yan'uwansu, su ɗari da ashirin da takwas ne gwarzayen sojoji ne. Shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim.

15. Na wajen Lawiyawa kuwa su ne Shemaiya ɗan Hasshub, jīkan Azrikam. Sauran kakanninsa su ne Hashabiya, da Bunni,

16. da Shabbetai, da Yozabad, ɗaya daga cikin manyan shugabanni na Lawiyawa, waɗanda suke lura da kewayen Haikalin Allah.

Karanta cikakken babi Neh 11